MDD

'Yan mata miliyan 11 za su yi ban-kwana da ilimi

Coronavirus ta dakatar da karatun dalibai a fadin duniya
Coronavirus ta dakatar da karatun dalibai a fadin duniya NTA.ng

Majalisar Dinkin Duniya ta ce akwai alamun yara mata miliyan 11 a kasashen duniya ba za su sake komawa makaranta ba bayan cire takunkumin da kasashe suka saka domin yaki da cutar korona da ke ci gaba da lakume rayuka.

Talla

Shugabar Hukumar UNESCO Audrey Azoulay ta bayyana haka inda ta ce suna matukar damuwar cewar rufe makarantu a kasashe da dama za su hana dalibai mata miliyan 11 samun ilimi saboda matsalolin da za su biyo baya.

Yayin da take ziyarar wata makaranta a Kinshasa na kasar Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo, Azoulay ta ce sun kaddamar da wani shirin wayar da kai domin ganin an bai wa daliban damar komawa karatu saboda muhimmancin samun ilimi.

Azoulay ta ce ilimin mata na da matukar muhimmanci ga hukumar UNESCO saboda ganin yadda aka bar su a baya a kasashe da dama.

Ministan ilimin kasar Congo Willy Bakonga ya bukaci taimakon hukumar wajen goyan bayan shirin shugaba Felix Tshisekedi na bai wa yara ilimi kyauta a makarantun firamare.

Masana sun ce gwamnatin Congo na kashe akalla Dala biliyan biyu da rabi wajen bai wa yara ilimin firamare kyauta a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.