Amurka-Zabe

Manyan Sanatocin Republican sun fara nesanta kan su da Trump gabanin Zabe

Shugaba Donald Trump yayin gangamin yakin neman zabensa a jihar Florida.
Shugaba Donald Trump yayin gangamin yakin neman zabensa a jihar Florida. SAUL LOEB / AFP

Yayin da ya rage kasa da makwanni 3 a gudanar da zaben shugaban kasar Amurka, jiga jigan 'yan Majalisar Dattawan Amurka da ke goyan bayan shugaba Donald Trump sau da kafa sun fara nesanta kan su da shugaban domin ganin sun kare kujerun su a zabe mai zuwa.

Talla

Ganin yadda 'yan Jam’iyyar Democrat suka tashi tsaye wajen tara makudan kudaden kamfe da kuma samun goyan bayan jama’a, shugabannin Sanataocin sun fara fitowa fili suna sukar jagorancin shugaba Trump da kuma nesanta kan su da shi, abinda ke nuna cewar da wuya shugaban ya kai labari a zaben watan gobe.

Sanata Ben Sasse na Jihar Nebraska yayin ganawa da jama’ar mazabar sa, ya caccaki yadda shugaban ya tinkari matsalar annobar korona inda ya zarge shi da kuma yadda ya rungumi masu nuna wariyar jinsi da nesanta kan sa daga halin da talakawa ke ciki.

Wannan matsayi na Sanata Sasse ya yi daidai da na Sanata Ted Cruz daga Jihar Texas wanda ya gargadi 'yan Jam’iyyar sa cewar suna iya fuskantar irin matsalar da aka samu lokacin abin kunyar ‘Watergate’ wadda za ta kaiga sun rasa kujerar shugaban kasa da kuma rinjayen da su ke da shi a zauren Majalisar Dattawa.

Shima Sanata Mitch McConnell, shugaban masu rinjaye a Majalisar Dattawa ya fito fili a ‘yan kwanakin nan yana sukar shugaban da kuma kin amincewa da shirin sa na amincewa da gagarumin tallafin agaji ga Amurkawa sakamakon cutar korona, abinda ke nuna raba hannun riga da shugaba Trump a bayyane, sabanin yadda aka saba ganin su.

Shima Sanata Lindsey Graham daga Jihar South Carolina da ke cikin 'yan gaba- gaba wajen goyan bayan duk manufofin da Donald Trump ya gabatar, yanzu haka kujerar sa na rawa, inda wani matashi bakar fata ke neman raba shi da majalisar.

Rahotanni sun ce, akwai alamu mai karfi da ke nuna cewar Jamie Harrison mai shekaru 44 na Jam’iyyar Democrat na iya kada Sanata Graham a zaben na watan gobe, wanda hakan zai bai wa bakaken fata biyu damar wakiltar jihar a zauren Majalisar Dattawa, duk da ya ke daya kujerar ta na hannun Jam’iyyar Republican ne.

Faduwar wadannan jiga jigan Jam’iyyar Republican ba karamar illa za ta yiwa Jam’iyyar su a Majalisa ba, yayin da kuri’un jin ra’ayin jama’a ke cigaba da bayyana Joe Biden a matsayin wanda ke sahun gaba wajen lashe zaben shugaban kasar na watan gobe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.