Azerbaijan-Armenia

Azerbaijan da Armenia sun karya yarjejeniyarsu

Kasashen biyu na zargin juna da yin barin wuta kan fararen hula.
Kasashen biyu na zargin juna da yin barin wuta kan fararen hula. Handout / Armenian Defence Ministry / AFP

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga kasashen Armenia da Azerbaijan da su mutunta sabuwar yarjejeniyar tsagaita musayar wuta, yayin da ta yi tur da hare-haren da bangarorin biyu suka kaddamar kan fararen hula.

Talla

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana takaicinsa kan yadda kasashen biyu ke far wa fararen hularsu, yana mai bada misali da harin ranar Asabar da ya kashe mutane 13 da suka hada da kananan yara bayan wani makami mai linzami ya dira kan gidaje a birnin Ganja na Azerbaijan.

Armenia da Azerbaijan sun cimma wata sabuwar yarjejeniya wadda ta fara aiki a tsakar daren da ya gabata, amma sai dai bangarorin biyu sun zargi juna da karya yarjejeniyar ta tsagaita musayar wuta.

Kasashen biyu sun dauki tsawon lokaci suna takun saka kan mallakar yankin Karabakh wanda ‘yan awaren Armenia da suka samu goyon bayan Yerevan suka karbe iko da shi a tsakanin shekarun 1990, lokacin da suka yi yakin da ya yi sanadiyar salwantar rayukan mutane kimain dubu 30.

Wannan yankin na Karabakh ya ayyana kansa a matsayin mai cikakken ‘yanci, amma babu wata kasa a duniya da ta amince da ikirarin samun ‘yancin, kuma har yanzu, dokokin kasa da kasa na kallon yankin a matsayin wani bangare na Azerbaijan.

Yanzu haka masu shiga tsakani na kasashen duniya na ci gaba da ganin sun shawo kan sabon rikicin da ya barke makwanni uku da suka gabata tsakanin kasashen biyu

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.