Coronavirus

Korona ta harbi mutane sama da miliyan 40

Coronavirus ta harbi mutane sama da miliyan 40 a sassan duniya.
Coronavirus ta harbi mutane sama da miliyan 40 a sassan duniya. REUTERS/Amanda Perobelli

Adadin mutanen da cutar coronavirus ta harba a sassan duniya ya haura miliyan 40, yayin da ta lakume rayuka fiye da miliyan 1 da dubu 114 tun bayan barkewarta a cikin watan Disamban bara a China.

Talla

Amurka ce kasar da coronavirus ta fi yi wa ta’adi domin kuwa ta kashe mutane dubu 219 da 676 a kasar kadai, yayin da Brazil ke matsayi na biyu da asarar mutane dubu 153 da 905, sai kuma India wadda ta rasa mutane dubu 114 da 610.

Cutar ta kashe mutane dubu 86 da 167 a Mexico , amma mutane dubu 43 da 646 ta halaka a Birtaniya.

Kasashen Turai sun fara daukar matakan dakile ci gaba da yaduwar cutar wadda ke neman sake ta’adi a karo na biyu, yayin da a baya-bayan nan Belgium ta rufe shagunan barasa da gidajen cin abinci na tsawon wata guda, baya ga kafa dokar hana fitar dare.

Shi ma Firaministan Italiya, Giuseppe Conte ya hana bude gidahen barasa da na cin abinci, sannan ya bayyana aniyar tilasta wa jama’a ci gaba da gudanar da ayyukansu a gidajensu.

Kazalika Wales za ta kafa cikakkiyar dokar kulle ta tsawon makwanni biyu daga ranar Juma’a da zummar rage yaduwar annobar.

Ko da yake birnin Melbourne wanda shi ne na biyu mafi girma a Australia, ya sassauta matakansa na kullen gida sakamakon raguwar cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.