Trump na gab da zare Sudan daga jerin kasashe masu daukar nauyin ta'addanci

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce a shirye ya ke ya cire sunan Sudan daga jerin kasashen da ke daukar nauyin ta’addanci, matakin da ke matsayin gagarumar nasara ga gwamnatin Sudan bayan cimma daidaito kan biyan diyyar Amurkawan da suka rasa rayukansu a harin Alqaeda na Ofishin jakadancin Amurkan da ke Kenya da Tanzania a 1998.

Shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump. Tom Brenner/Reuters
Talla

Trump wanda ke sanar da wannan mataki a sakon da ya wallafa ta shafinsa na Twitter, ya ce gwamnatin ta Sudan ta amince da biyan kunshin dala biliyan 335 matsayin diyyar rayukan Amurkawan.

Trump matukar Sudan ta kammala tura kudin ko shakka babu za ta fice daga jerin kasashe masu daukar nauyin ayyukan ta’addanci, matakin da tuni ya samu goyon bayan kungiyar Tarayyar Turai.

Sudan dai na cikin jerin kasashe 4 da Amurka ta sanya a jerin masu daukar nauyin ayyukan ta’addanci ciki har da Korea ta Arewa da Syria, bayanda ta bayar da mafaka ga Osama bin Laden da ke matsayin jagoramn Alqaeda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI