Zaben - Amurka

Sama da mutane miliyan 50 sun kada kuri'un su gabanin zaben Amurka

Masu kada kuri'u a zaben Amurka
Masu kada kuri'u a zaben Amurka REUTERS/Micah Green

Masu sa' ido kan zaben Amurka sun bayyana cewar ya zuwa yanzu mutane sama da miliyan 50 sun riga sun kada kuri’ar su a zaben da ake fafatawa tsakanin shugaba Donald Trump da tsohon mataimakin shugaban kasa Joe Biden.

Talla

Kungiyar da ake kira ‘US Election Project’ dake karkashin Jami’ar Florida tace Amurkawa miliyan 35 suka aike da kuri’un su ta gidan waya, yayin da sama da miliyan 15 suka kada kuri’u da kan su a tashoshin zabe.

Wannan adadi ya zarce na shekarar 2016 inda aka samu mutane miliyan 47 sun kada kuri’a mako guda kafin gudanar da zabe.

Dokar kada kuri’a da wuri dai ya banban ta tsakanin Jiha zuwa Jiha a Amurka, inda Jihar New York, daya daga cikin jihohin da suka fi yawan jama’a zasu fara nasu daga ranar asabar, abinda ake ganin zai kara yawan mutanen da zasu kada kuri’u kafin ranar 3 ga watan gobe.

Yan Jam’iyyar Democrat, cikin su harda tsohon shugaban kasa Barack Obama sun bukaci magoya bayan su da su je su kada kuri’un su da wuri.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.