Nukiliya

Kasashe 50 sun sa hannu a yarjejeniyar haramta amfani da makamin Nukiliya

Sashen makamin Nukiliyar Iran.
Sashen makamin Nukiliyar Iran. AFP/HAMED MALEKPOUR

Honduras ta zama kasa ta 50 da ta rattaba hannu kan yarjejeniyar kasa da kasa da ke haramta amfani da makamin nukiliya, matakin da zai bada damar fara aiwatar da yarjejeniyar nan da kwanaki 90.

Talla

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana rattaba hannun kan yarjejeniyar a matsayin wani mataki na kawo karshen fafutukar kasashen duniya game da janyo hankali kan irin barnar da makamin nukiliya ke yi wa bil’adama.

Guterres ya kara da cewa, matakin wani yunkuri ne na soke nukiliya baki dayanta, yana mai cewa, wannan shi ne babban kudirin da Majalisar Dinkin Duniya ta sanya a gaba a yanzu dangane da kwance damarar makamai.

Tuni kungiyoyin agaji da suka hada da ICAN mai fafutukar kawo karshen makaman nukiliya suka yi maraba da batun.

Shugaban Kungiyar Agaji ta Red Cross, Peter Maurer ya ce, wannan rana ce ta samun nasara ga bil’adama wadda kuma ke nuni da samun makoma mara hadari.

Sai dai har yanzu manyan kasashen duniya masu karfin makaman nukiliya da suka hada da Amurka, Rasha, China da Birtaniya baya ga Faransa ba su sanya hannu kan wanna yarjejeniya ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.