Amurka

Larabawa sun fi goyon bayan Biden fiye da Trump a zaben Amurka- Bincike

Wani Bincike ya nuna cewar kasashen Larabawa sun fi son tsohon mataimakin shugaban Amurka Joe Biden ya lashe zaben da za a yi watan gobe maimakon shugaba Donald Trump.

'Yan takarar shugaban kasa a zaben Amurka, Shugaba Donald Trump na Republican da Joe Biden na Jam'iyyar Democrat kuma tsohon mataimakin shugaban kasar.
'Yan takarar shugaban kasa a zaben Amurka, Shugaba Donald Trump na Republican da Joe Biden na Jam'iyyar Democrat kuma tsohon mataimakin shugaban kasar. AP/Patrick Semansky
Talla

Binciken da Jaridar Arab News ta wallafa wanda wani kamfanin Birtaniya ya gudanar, ya ce daga cikin mutane 3,097 daga kasashen Gabas ta tsakiya da Arewacin Afirka da aka tintiba, kashi 39 sun bayyana goyan bayan su ga Biden, yayin da kasha 12 suka goyi bayan Trump.

Yayin da aka tambaye su, ko wane shugaba suke gani zai fi kima ga muradun kasashen Larabawa, kashi 49 sun ce babu ko daya daga cikin su, amma kuma suna da yakinin cewar Biden zai fi dangantaka mai kyau da kasashen na su.

Har yanzu dai Biden ke kan gaba a yawan magoya baya a kasar ta Amurka dai dai lokacin da zaben na watan Nuwamba ke ci gaba da karatowa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI