Amurka

Amurkawa miliyan 70 sun kada kuri'un gabanin ranar zabe

Fiye da mutane miliyan 70 ne suka kada kuri'a a zaben gabanin ranar 3 ga watan Nuwamba da za a yi zaben gamayya.
Fiye da mutane miliyan 70 ne suka kada kuri'a a zaben gabanin ranar 3 ga watan Nuwamba da za a yi zaben gamayya. REUTERS

Rahotanni daga Amurka na nuna cewa jumullar mutane miliyan 70 ne suka kada kuri’unzu kawo yanzu adadin da ke matsayin rabin yawan mutanen da suka kada kuri’a a zaben shugaban kasa na 2016.

Talla

Zaben wanda za akara tsakanin shugaba mai ci Donald Trump na jam’iyyar Republican da dan takarar jam’iyyar Democrat Joe Biden tsohon shugaban kasar, ‘yan takarar biyu na ci gaba da gangamin yakin neman zabe da nufin samun damar darewa madafun iko.

A jiya Talata, Biden ya gudanar da wani gagarumin gangami a Georgia jihar da ake ganin Democrat za ta iya kwace kujerar Republican, inda yayin gangamin Biden ke ci gaba da sukar Trump kan sakacin da ya yi na tunkarar annobar coronavirus da ta salwantar da tarin rayukan Amurkawa.

Shima dai Donald Trump wanda ya gudanar da makamancin gangamina Michigan da Wiconsin da kuma Nebraska ya diga ayar tambaya kan yiwuwar tabbatar da adalci a zaben na watan gobe.

Ko a yau Laraba Trump zai kuma gadanar da wani gangami na daban a Arizona jihar da Biden ke da cikakken goyon baya.

Haka zalika duk dai a yau Larabar, Joe Biden zai gabatar da jawabi daga gidansa kan matakan da ya ke shirin dauka don yakar Covid-19 dama inganta bangaren lafiyar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.