Amurka

Google, Facebook da Twitter sun gurfana gaban Majalisar Amurka kan labaran karya

Tambarin kamfanonin shafukan sada zumunta na Facebook, Amazon, Apple da Google.
Tambarin kamfanonin shafukan sada zumunta na Facebook, Amazon, Apple da Google. REUTERS/File Photo

Shugabannin shafukan sada zumunta ciki har da na Facebook, Twitter da Google sun gurfana gaban Majalisar Amurka don amsa tambaya kan yadda su ke bayar da damar bazuwar labarai marasa tushe da na tunuzra al’umma a shafukansu.

Talla

Kamfanonin kafafen dai na fuskantar matsin lamba daga Majalisar Amurkan wajen ganin sun taka muhimmiyar rawa don hana yaduwar labarai marasa tushe yayin zaben kasar da ke tunkarowa a makon farko na wata mai kamawa.

Kwamitin kasuwanci na Majalisar Dattijan za ta yi doguwar ganawa da shugaban Facebook Mark Zuckerberg da na Twitter Jack Dorsey da kuma Sundar Pichai daga Google.

Yayin ganawar kamfanonin za su fayyacewa majalisar irin matakan da suka shirya dauka don ganin an yi amfani da doka wajen yada sahihan labarai a shafukan nasu.

Karkashin tanadin doka dai, Kamfanonin ba su da hurumin iya sauyawa ko kuma goge wani sako ko rubutu da masu amfani da shafukan suka wallafa, duk da yak e akwai masu goyon bayan ganin kamfanonin na gogewar don dakile kalaman batanci da na tunzura al’umma da kuma labaran karya.

Sai jam’iyyun Democrat da Republican na kalubalantar shafi na 230 na kundin tsarin mulkin Amurka da ke kokarin iyakance irin kalaman da za a iya

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI