Saudiya-Iran

Saudiya da Iran sun caccaki Macron kan batanci ga addinin Islama

Sarki Salman bin Abdulaziz na Saudiya.
Sarki Salman bin Abdulaziz na Saudiya. Bandar Al-Jaloud/Saudi Royal Palace/AFP

Kasashen saudiya da Iran sun yi kakkausar suka ga matakin shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron na goyon bayan zanen batancin da aka yiwa fiyayyen halitta annabin rahma tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi.

Talla

Kasashen biyu da ke matsayin jagororin musulmi na fitar da wannan sanarwar ne dai dai lokacin da zanga-zangar kyamar Faransa ke ci gaba da karfi a sassan duniya musamman kasashen da musulmi ke da rinjaye.

Zuwa yanzu dai Tuni wasu kasashe suka rungumi akidar daina hulda ko kuma sayen duk wani kaya daya fito daga kasar ta Faransa.

Saudiya wadda ke matsayin jagorar musulmi mabiya Sunnah, ta ce ko kadan matakin na Macron bai yi kamanceceniya da dokar fadar albarkacin baki da kuma cin zarafin addini da kundin tsarin mulkin kasar ya tanadar ba.

Cikin sanarwar ma'aikatar harkokin wajen Saudiya ta ce duk da ya ke kundin tsarin mulkin na Faransa ya tanadi wannana matsaya amma sam kalaman da Emmanuel Macron ya furta a matsayinsa na shugaban kasa bai kamace shi ba.

A bangare guda tuni Iran ta yi sammacin jakadan Faransa a Tehran don amsa mata tambayoyi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.