Mauludi

Al'ummar Musulmi na bikin ranar Mauludi a sassan Duniya

Wasu daga cikin masu murnar Zagayowar Ranar Haihuwar Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad (SAW) a birnin Legas da ke Najeriya.
Wasu daga cikin masu murnar Zagayowar Ranar Haihuwar Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad (SAW) a birnin Legas da ke Najeriya.

Yau Alhamis 29 ga watan Oktoban 2020 Al’ummar Musulmi a sassan Duniya ke bikin murnar zagayowar ranar 12 ga watan Rabi’ul Awwal ranar da ake dangantawa da haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi.

Talla

Yayin bikin Mauludin dai bisa al’ada Musulmin galibi mabiya Sufaye kan yi dafifi tare da yawaita zikiri salatin Annabi baya ga mabanbantan kasidun yabo ga fiyayyen halitta.

Gabanin ranar Mauludin dai, kamar yadda Musulmi kan yi bukukuwan Sallah, Iyaye kan yiwa yaransu sabbin dinkuna yayinda mawadata ke yanka raguna da shanu don hidimar ranar da ake yiwa gagarumin biki.

Wasu bayanai na nuna cewa hatta a cikin gidaje Mata kan girka kalolin abinci na alfarma tare da rarrabawa sadaka duk dai a kokarin girmama ranar.

Kalmar Mauludin wadda ta samo asali daga Larabci da ke nufin ‘‘haihuwa’’ a wasu yarukan na da sunaye daban kamar Havliye, Donba da kuma Gani kamar yadda wasu kan kira ranar ta Mauludi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.