Majalisar Dinkin Duniya

Guterres ya koka da rashin sanya Mata cikin aikin samar da zaman lafiya

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres.
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres. REUTERS/Lisi Niesner

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana damuwa kan rashin samun Mata da yawa wajen aikin samar da zaman lafiya, shekaru 20 bayan kwamitin sulhu ya amince da amfani da su a cikin shirin.

Talla

Guteres ya ce akwai sauye sauye da dama da aka yi tun bayan amincewa da kudirin na 1325 a shekara ta 2000 wanda ya karfafa masu ruwa da tsaki wajen bai wa mata damar taka rawa wajen aikin samar da zaman lafiya da kuma tattaunawa wajen kawo karshen tashin hankali da aikin jinkai.

Sakataren ya ce mazaje sun mamaye fage da dama da suka shafi jagoranci, yayin da kasha 7 na mata ne kawai ke jagorancin kasashe, sai kuma mazaje suka mamaye sauran.

Guterres ya bayyana yadda ake watsi da mata wajen yunkurin diflomasiya na sasanta rikicin kasashen Afghanistan da Mali da kuma Yemen, inda ya bukaci sake tunani akai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.