Amurka

Tsaffin manyan Lauyoyin Amurka sun goyi bayan Biden tare da sukar Trump

'Yan takarar shugabancin kasar Amurka, shugaba mai ci Donald Trump na Republican da Joe Biden na Democrat.
'Yan takarar shugabancin kasar Amurka, shugaba mai ci Donald Trump na Republican da Joe Biden na Democrat. REUTERS

Tsoffin Manyan Lauyoyin Gwamnatin Amurka da shugabannin Jam’iyyar Republican suka nada su aiki, sun fito fili sun yi tir da jagorancin shugaba Donald Trump saboda yadda ya jefa harkokin siyasa kan bangaren shari’a, inda suka bayyana goyan bayan su ga takarar Joe Biden na Jam’iyyar Democrat.

Talla

A budaddiyar wasikar da suka rubuta, manyan lauyoyin sun cacaki shugaba Trump wanda suka bayyana shi a matsayin wanda ke bukatar ma’aikatan shari’a suma masa aikin da yake so domin biyan bukatar kan sa da na siyasar sa, kamar zargin sanya hannun kasashen waje cikin zaben kasar da kuma shari’ar da ta shafi na kusa da shugaban kana da matakan da ake dauka domin kare martabar bangaren shari’a.

Wasikar wanda Dwight Eisenhower, mai gabatar da kara lokacin gwamnatin shugaba George Bush ya sanyawa hannu ta bayyana mulkin shugaba Donald Trump a matsayin babbar barazana ga bin doka da oda a kasar Amurka.

Lauyoyin sun bayyana Joe Biden a matsayin wanda ya sadaukar da rayuwar sa wajen mutunta dokokin Amurka da kare ‘yancin bangaren shari’a da kuma tabbatar da ganin gwamnatin tarayya tayi amfani da karfin doka ba tare da nuna banbanci ga wani bangare na Amurkawa ba.

Lauyoyin sun kuma yabawa Biden kan yadda ya fahimci hadin kan kasa maimako rarraba kan jama’a, inda suka bayyana shi a matsayin wanda zai iya magance matsalolin da suka addabi kasar.

Wasikar ta bayyana goyan bayan lauyoyin ga takarar Biden wanda suka ce zai yi kokarin hada kan jama’a da kuma kare dokokin kasa wadanda suka kare duk wani BaAmurke da kuma baiwa bangaren shari’a damar sauke nauyin dake kan ta.

A watan Agusta da ta gabata, tsohon shugaban hukumar leken asirin Amurka ta CIA Michael Hayden da tsohon Sakataren Tsaro Chuck Hagel na daga cikin tsoffin sakatarorin tsaron kasar 74 da suka sanya hannu kan wasikar dake cewa ba zasu goyi bayan Donald Trump a zabe mai zuwa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.