'Yancirani

'Yancirani kusan 140 sun nutse cikin teku a kokarinsu na shiga Turai

Sauran 'yanciranin da aka yi nasarar cetowa.
Sauran 'yanciranin da aka yi nasarar cetowa. MV Louise Michel/Handout via REUTERS

Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla bakin haure da ke cikin kwale kwale akalla 140 suka nutse a gabar ruwan kasar Senegal lokacin da suke kan hanyar zuwa kasashen Turai.

Talla

Hukumar kula da kaurar baki ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce daga cikin mutane kusan 200 da ke cikin kwale kwalen, kusan 60 ne aka iya cetowa, yayinda 140 suka bata.

Rahotanni sun ce bakin na bukatar zuwa tsibirin Canary da ke Spain ne lokacin da aka samu hadarin.

Jami’in hukumar Bakary Doumbia ya bukaci taimakon gwamnatoci da kasashen duniya wajen ganin sun dakile mutanen da ke sarrafa irin wannan baki da ke neman isa Turai ta kowacce hanya.

Gwamnatin kasar Spain ta ce akalla baki 11,000 suka isa gabar ruwan ta a cikin wannan shekara sabanin 2,557 da aka samu bara.

Hukumar ta ce mutane 414 suka mutu a cikin wannan shekara sakamakon hadarin da ake samu a cikin teku daga irin wadannan mutane da ke neman tsallakawa Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.