Obama-Trump

Obama ya caccaki Trump da kalami mafi zafi a yakin neman zaben Biden

Tsohon shugaban Amurka Barack Obama ya cacaki wanda ya gaje shi shugaba Donald Trump, a suka mafi girma tun bayan fara yakin neman zaben shugaban kasar da za’ayi ranar talata mai zuwa.

Tsohon shugaban kasar Amurka Barack Obama da dantakarar shugabancin kasar Joe Biden.
Tsohon shugaban kasar Amurka Barack Obama da dantakarar shugabancin kasar Joe Biden. REUTERS/Jim Bourg
Talla

Yayin da ya jagorancin yakin neman zaben Joe Biden dan takarar Jam’iyyar Democrat a karshen mako, Obama ya bayyana Trump a matsayin wanda ya damu da kan sa kawai sabanin bukatun miliyoyin Amurkawar da yake jagoranci.

Obama yace yayin da shugaba Trump ya sanya bukatun sa da kimar sa a gaba, Joe Biden ya damu da halin da Amurkawa da iyalan su ke ciki.

Tsohon shugaban ya cacaki Trump kan yadda yake sukar kafofin yada labarai kan yadda suke yada labaran illar da cutar korona ke yiwa jama’ar kasar da kuma yadda ya mayar da hankalin sa kan yawan jama’a a wurin gangamin sa.

Obama yace har yanzu Trump na fushi kan cewar yawan jama’ar da suka halarci bikin rantsar da shi basu kai yawan na shi (Obama) ba lokacin da ya sha ranstuwar kama aiki bayan zaben shi zagaye na farko, inda yayi tambayar cewar ko bas hi da wani abinda zai mayar da hankali akai sai wannan ne.

Tsohon shugaban yace Trump yana bukatar samun yabo daga jama’a kan nasarar tattalin arzikin da ya gada, amma kuma baya son daukar alhakin mutuwar Amurka sama da 220,000 sakamakon cutar korona, inda yace wannan ba shugabanci na gari bane.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI