Ana kashe akalla dan jarida guda a duk kwanaki 4 a duniya - MDD

Wasu 'yan jaridu a kasar Afghanistan
Wasu 'yan jaridu a kasar Afghanistan AFP/Shah Marai

Wani rahotan Majalisar Dinkin Duniya yace rayuwar Yan Jaridun dake fallasa labarin cin hanci da rashawa ko kuma cin zarafin Bil Adama yafi hadari sabanin wadanda ke dauko rahoto daga filin yaki, matsalar dake tada hankali sosai.

Talla

Hukumar UNESCO dake sanya ido kan harkokin Yan Jaridu tace Yan Jaridu 99 aka kashe a duniya a shekarar 2018, yayin da aka kashe 57 a shekarar 2019.

Rahotan yace adadin mutane 57 da aka kashe bara shine mafi karanci a cikin shekaru 10 da suka gabata, abinda ke nuna irin ukubar da Yan Jaridu ke fuskanta wajen gudanar da ayyukan su.

Majalisar tace yayin da alkaluman suka ragu a bara, barazanar da ake yiwa Yan Jaridun na karuwa, yayin da ake sauya dabarun kai musu hari.

UNESCO tace adadin Yan Jaridun dake mutuwa a filin yaki yayi matukar raguwa, yayin da akasarin wadanda ake hallakawa basu da nasaba da kasashen dake fama da rikici.

Rahotan yace kashi 31 na hare haren da ake kaiwa Yan Jaridu an same su ne a kasashen dake Yankin Amurka ta Kudu da Yankin Caribbean, yayin da aka samu kasha 30 a yankin Asia.

kasar Mexico ke sahun gaba wajen yawan Yan Jaridun da aka kasha wadanda ke rahoto kan masu hada hadar miyagun kwayoyi, inda a bara aka kasha 12, sai Syria inda aka kashe 6.

Rahotan ya kuma ce Yan Jaridu mata suma suna fuskantar barazana wajen cin zarafin su da kuma jikkata su, yayin da rahotan ke cewa ana kasha dan jarida guda a cikin ko wadanne kwanaki 4 a cikin shekaru 10 da suka gabata.

Kungiyar dake sanya ido kan harkokin Yan Jaridu da kuma kare su ta RSF ta bukaci Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres da ya kirkiro ofishin mai kula da tsaron Yan Jaridu a Majalisar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.