Zaben - Amurka

Trump ya yi watsi da kuri'ur jin ra'ayin jama'a dake nuna zai sha kaye

Shugaban Amurka Donald Trump yayin gangamin siyasa a Ohio
Shugaban Amurka Donald Trump yayin gangamin siyasa a Ohio REUTERS/Tom Brenner

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi watsi da kuri’un jin ra’ayin jama’ar dake nuna cewar abokin karawar sa Joe Biden na Jam’iyyar Democrat ya kama hanyar lashe zaben shugaban kasar da za’ayi gobe Talata.

Talla

Yayin da yake jawabi ga taron magoya bayan sa a Fayetteville dake North Carolina, Trump ya bayyana sakamakon kuri’un a matsayin labaran karya, inda yake cewa babu abinda zai hana shi samun nasara.

Rahotanni sun ce yanzu haka da dama daga cikin magoya bayan Jam’iyyar Republican suna cikin fushi inda suke yiwa kowa shagube, daga yan jaridu zuwa shugabannin kafofin sada zumunta da Hillary Clinton da ta kara da Trump a shekarar 2016 da kuma Yan Majalisun Democrat, saboda fargabar da Trump ke da shi na faduwa zaben gobe.

Dan takarar Democrat Joe Biden na cigaba da samun tagomashi a jihohi da dama cikin su harda wadanda suka fi muhimmanci a zaben na Amurka, cikin su harda Georgia da Texas.

Yayin jawabi ga magoya bayan sa a Cleveland dake Jihar Ohio, Biden ya bukaci Trump ya tattara kayan sa domin barin fadar shugaban kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.