Amurka-Zabe

Amurkawa na kada kuri'a a babban zaben kasar

Yau al’ummar kasar Amurka ke gudanar da zaben shugaban kasa wanda ake fafatawa tsakanin shugaba Donald Trump dake neman wa’adi na biyu a karkashin Jam’iyyar sa ta Republican da toshon mataimakin shugaban kasa Joe Biden da Jam’iyyar Democrat ta tsayar takara.

Trump da Biden na fafatawa a zaben Amurka.
Trump da Biden na fafatawa a zaben Amurka. JIM WATSON, SAUL LOEB / AFP
Talla

Zaben na bana na dauke hankalin mazauna ciki da wajen Amurka saboda taka rawar da shugaba Donald Trump ya yi a shekaru 4 da suka gabata, bayan ya kada Hillary Clinton da ta fafata da shi a shekarar 2016.

Masu zaben na duba batutuwa da dama da suka hada da tattalin arzikin kasar a karkashin shugaba Trump da yadda Amurkawa sama da 225,000 suka mutu sakamakon annobar korona da yadda Amurka ke takun saka da manyan kawayen ta musamman daga kasashen Turai da batun nuna wariyar jinsi da ya dada kamari a cikin kasar da kuma yadda 'yan sanda ke cigaba da hallaka bakaken fata.

Duk da nasarar da shugaba Trump ya samu a bangaren tattalin arziki, shirin sa na Amurka a farko na cigaba da samun suka musamman daga abokan adawar sa da kuma kawayen kasar da ke sassan duniya.

Wannan ya sa dan takarar Jam’iyyar Democrat Joe Biden ke samun tagomashi a takarar zaben da ya ke yi da Trump wanda kuri’un jin ra’ayin jama’a da dama ke sa shi samun gaba da shugaba Donald Trump mai ci.

Biden ya sha alwashin sake alkiblar Amurka da ta sha banban da mulkin Trump wajen hada kan jama’ar kasar ba tare da nuna banbancin launin fata ba da amfani da masana kimiyya wajen shawo kan cutar korona wadda ta kashe Amurkawa da dama da mayar da kasar cikin jerin kasashen da ke magance gurbata muhalli da kuma bunkasa tattalin arzikin kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI