Amurka-Jamus

Jamus ta gargadi Amurka kan yiwuwar fadawa rikicin siyasa

Wasu al'ummar Amurka da ke gangami gabanin fitar sakamakon zabe a yammacin yau Laraba.
Wasu al'ummar Amurka da ke gangami gabanin fitar sakamakon zabe a yammacin yau Laraba. REUTERS/Cheriss May

Kasashen duniya sun mayar da martani game da zaben Amurka, inda Jamus ta yi gargadin cewa, kasar na fuskantar barazanar rikici bayan shugaba Donald Trump ya ayyana kansa a matsayin wanda ya yi nasara tare da fadin cewa, zai garzaya kotun koli don dakatar da tattara sakamakon zaben.

Talla

Ministar tsaron Jamus Annegret Kramp Karrenbauer ta shaidawa manema labarai cewa, kawo yanzu ba a tabbatar da wanda ya yi nasara a zaben ba a hukumance, kuma ana kan kidaya kuri’un da aka kada.

Ministar ta kara da cewa, akwai yiwuwar shugaba Donald Trump ya haddasa rikicin kundin tsarin mulki a Amurka, tana mai bayyana wannan lamari a matsayin abin da ya shafe su.

Kazalika Ministar wadda kuma ita ce, shugabar jam’iyyar Angela Merkel ta ce, alakar Amurka da Jamus ta gamu da ibtila’i a cikin shekaru hudu da Trump ya kwashe yana mulki, inda ya ke caccakar gwamnatin Berlin kan lamurran da suka shafi kasuwanci da ayyukan soji.

Sai dai a bangare guda, Firaministan Slovenia, Janes Jansa mai ra’ayin rikau, ya taya shugaba Trump murnar samun nasarar sake zabensa don yin wa’adi na biyu a Fadar White House.

Wannan kuwa na zuwa ne duk da cewa, babu wanda aka ayyana a hukumance a matsayin wanda ya yi nasara tsakanin Trump da Joe Biden.

A cewar Firaministan, a bayyana ta ke cewa, Amurkawa sun sake zaben shugaba Trump.

Har yanzu dai ana dakon kammala tattara sakamakon wasu jihohi a zaben na Amurka, yayin da alkaluman da ake da su a yanzu suka nuna cewa Biden na sahun gaba da yawan kuri’u.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.