Amurka

Dan takarar shugaban kasa a Amurka Kanye West ya samu kuri'u dubu 60

Yayinda hankalin Duniya ya koma kan fafatawar da ake tsakanin shugaba Donald Trump da Joe biden domin ganin wanda zai lashe zaben Amurka da ake tababa akai, masu sanya ido sun kawar da kan su daga sauran yan takarar da suka nemi shugabancin kasar.

Kanye West guda cikin 'yan takarar shugabancin Amurka.
Kanye West guda cikin 'yan takarar shugabancin Amurka. REUTERS/Randall Hill
Talla

Daya daga cikin wadanda suka tsaya takara shi ne fitaccen mawakin kasar Kanye West wanda ya tsaya a matsayin dan takarar indifenda ya kuma samu kuri’u akalla dubu 60 cikin jihohin kasar 12 da aka sanya sunansa a matsayin dan takara.

Rahotanni sun bayyana cewar West ya samu kuri’a mafi yawa ne da suka kai 10,000 a Jihar Tennesse kamar yadda Jaridar New York Times ta wallafa.

West wanda ya godewa magoya bayan sa ya bayyana alamar sake takara a shekarar 2024 kamar yadda ya aike ta kafar twitter.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI