Amurka

Masoyan Biden sun fara ruguntsumi a fadar White House

Magoya bayan Biden dauke da allunan da ke sukar Trump
Magoya bayan Biden dauke da allunan da ke sukar Trump Reuters

Daruruwan magoya bayan Joe Biden sun yi dandazo a harabar fadar White House suna buga manyan ganguna tare da raye-raye, a daidai lokacin da suke ganin cewa, dan takararsu ne zai lashe zaben shugabancin Amurka.

Talla

Koda yake wasu daga cikin magoya bayan sun bayyana damuwa kan cewa, shugaba Donald Trump ka iya yin gaban kansa wajen ayyana kansa a matsayin wanda ya yi nasara a zaben.

An dasa manyan shingaye domin dakile masu ruguntsumin, yayin da jami’an ‘yan sanda suka zura musu ido, amma babu wata alamar tashin hankali.

Daya daga cikin magoya bayan, Malik Williams ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP cewa, ya halarci gangamin ne domin nuna farin cikinsa saboda a cewarsa, nan kusa Trump zai tarkata kayansa ya yi ban-kwana da fadar White House.

Ana ci gaba da tattara sakamakon zaben kasar, inda kawo yanzu Trump ke kan gaba da yawan kuri’un gama-gari, amma Joe Biden ya ba shi tazara wajen samun yawan mambobin kwamitin zaben shugaban kasa.

A zahiri, yawan kuri’un gama-gari ba shi da wani tasiri a zaben na Amurka, inda kowanne dan takara ke fatan samun yawan wakilan da ke zaben shugaban kasa fiye da yawan kuri'u.

Wadannan wakilai da ake kira 'Electoral College' su ke da alhakin karshe na tantance wanda zai zama shugaban kasa a Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.