Amurka-Zabe

Republican da Democrat na shirin yin kankankan a Majalisar Dattijan Amurka

Zuwa yanzu dai kowacce cikin jam'iyyun biyu na da kujeru 47, sai dai Biden na gaban Trump ta fuskar yawan kuri'a dama yawan wakilan da za su tantance shugaban kasa.
Zuwa yanzu dai kowacce cikin jam'iyyun biyu na da kujeru 47, sai dai Biden na gaban Trump ta fuskar yawan kuri'a dama yawan wakilan da za su tantance shugaban kasa. ion Night watch party and drag show, Tuesday, Nov. 3, 2020, in t

Duk da gagarumar nasarar da jam’iyyar Democrat ta samu wajen sake mamaye kujerun majalisar wakilan Amurka, har yanzu babu tabbacin bangaren da zai yi rinjaye a Majalisar Dattijai.

Talla

Zuwa yanzu dai Jam’iyyar Democrat ta kwace kujerun majalisar dattijai 2 daga hannun Republican wato na yammacin Colorado da kuma Arizona duk da cewa har yanzu akwai shakkun gibin akalla kujeru 3 zuwa 4 da za su hana jam’iyyar jagorancin Majalisar wakilan.

Kowanne bangare tsakanin jam’iyyun biyu na Republican da Democrat na da kujeru 47 cikin gurbi 99 da ake da su gabanin zaben cike gurbi a watan Janairu, wanda ke nuna cewa duk wacce ta samu kujeru 51 a zaben kai tsaye ita ke da rinjayen Majalisar ta Dattijai.

Yanzu haka dai idon jam’iyyar Democrat na kan Maine da Georgia inda Sanata Susan Collins ta Republican ke jagoranci da karin kashi 7 sai kuma Jon Ossoff da shima ke jagorancin Georgia da kashi 90 na yawan kuri’un da aka kirga, wanda ke nuna idan har Democrat za ta iya lashe 1 daga cikin kujerun za ta yi samun rinjaye a zauren majalisar dattijan.

Matukar dai aka yi canjaras a yawan kujerun da jam’iyyun biyu suka samu na Majalisar Dattijai, kenan babu jam’iyyar da za a tabbatar a matsayin mai rinjaye a majalisar har sai bayan zaben cike gurbin ranar 5 ga watan Janairun badi na dayar kujerar sanatan na Georgia.

Shima dai Sanata Lindsley Graham na Republican ya yi nasarar komawa majalisar duk da shakkun da ya dabaibaye makomarsa makwanni 2 gabanin zaben inda yak ara da Jaime Harrison bakar fata a South Carolina.

A bangare guda Republican ta yi awon gaba da kujerar Democrat a Alabama bayan na Texas Iowa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.