Amurka

Trump ya bukaci a sake kirga kuri'un Wisconsin

Shugaban Amurka Donald Trump ya bukaci hukumar zaben kasar da ta sake kidaya kuri’un Jihar Wisconsin wanda alamu suka nuna cewar Joe Biden na Jam’iyyar Democrat ya kama hanyar lashewa da gagarumar rinjaye.

Shugaba Donald Trump na Amurka.
Shugaba Donald Trump na Amurka. REUTERS/Tom Brenner
Talla

Manajan yakin neman zaben Trump Bill Stephen ya sanar da haka inda ya ce suna zargin an tafka magudi a yankunan Jihar da dama da suka jefa shakku kan sakamakon zaben, yayin da shugaba Trump ya kama hanyar samun nasara.

Jihar Wisconsin na daya daga cikin manyan jihohin da ke iya sauya sakamakon zaben.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI