Zaben - Amurka

Zan ruga kotun koli muddin aka ce na fadi zabe - Trump

Shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump. Tom Brenner/Reuters

Shugaban Amurka Donald Trump yace muddin aka bayyana cewar ya fadi zaben shugaban kasar da akayi zai ruga kotun koli domin kalubalantar sakamakon sa.

Talla

Yayin jawabi ga magoya bayan sa, Trump wanda yace yana da yakinin samun nasarar zaben yace koda sunan wasa ba zai amince da sakamakon sa ba idan aka ce dan takaran Democrat Joe Biden ya samu nasara akan sa.

Ya zuwa yanzu sakamakon da aka gabatar ya nuna cewar Joe Biden ke sahun gaba wajen lashe wannan zabe, ganin yadda ya samu kujerun wakilai 225 sabanin Trump wanda ya samu 213.

Ana saran wanda zai samu nasarar zaben ya samu kujeru 270.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.