Amurka-Biden

Zan mayar da Amurka cikin yarjejeniyar yanayi ta Paris- Biden

Dan takarar shugabancin Amurka Joe Biden.
Dan takarar shugabancin Amurka Joe Biden. AP/Carolyn Kaster

Tsohon Mataimakin shugaban kasar Amurka kuma wanda ke sahun gaba wajen lashe zaben shugaban kasa Joe Biden ya bayyana cewar a ranar farko da zai shiga office zai mayar da Amurkar cikin yarjejeniyar magance gurbacewar muhalli da shugaba Donald Trump ya cire kasar daga ciki.

Talla

A sakon da ya aike ta kafar twitter, Biden ya ce yau gwamnatin Trump ta janye daga yarjejeniyar Paris, kuma da ya rage kwanaki 77 dokar ta fara aiki, gwamnatin Biden za ta mayar da kasar ciki.

Sauyin yanayi dai na daya daga cikin manyan batutuwan da suka mamaye zaben Amurka.

A wani jawabinsa na daban ga magoya bayansa cikin daren jiya Laraba dan takarar shugaban Amurka Joe Biden ya bayyana farin cikin sa da irin nasarar da ya ke samu a sakamakon zaben da ake cigaba da kidayawa.

A takaitaccen jawabin da ya yiwa magoya bayan sa, Biden ya ce idan suka samu nasara zasu zama na 4 kenan a tarihin kasar da suka kawar da gwamnati mai ci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.