Bakonmu a Yau

Tattaunawa da Dr Yakubu Haruna Ja'e kan darussan da ya kamata Duniya ta koya daga zaben Amurka

Sauti 03:56
Ana ci gaba da dakon sakamakon zabe a Amurka.
Ana ci gaba da dakon sakamakon zabe a Amurka. AFP

Har yanzu dai ana ci gaba da dakon sakamakon zaben shugaban kasar Amurka wanda ya dau hankalin ilahirin kassshen duniya, duba da kimar Amurka a matsayinta ta kasar da ake koyi da ita a harkar dimokaradiyya.Michael Kuduson ya tattauna da Dokta Yakubu Haruna Ja’e, na sahen kimiyyar siyasa a Jami’ar jihar Kaduna a Najeriya, wanda ya yi tsokaci a kan abubuwan da ke gudana da ma abin da za a koya daga wannan zabe.