WTO-Amurka

An dage taron zaben shugaban WTO

Amurka ta ki goyon bayan Ngozi Okonjo-Iweala don zama sabuwar shugabar Hukumar Kasuwanci ta Duniya.
Amurka ta ki goyon bayan Ngozi Okonjo-Iweala don zama sabuwar shugabar Hukumar Kasuwanci ta Duniya. AFP Photos/Fafbrice Coffrini

Hukumar Kula Kasuwanci ta Duniya ta dage taron da ta shirya gudanarwa makon gobe domin zaben wanda zai zama  sabon shugabanta sakamakon hawa kujerar naki da Amurka ta yi kan wadda ake sa ran ta zama shugabar Ngozi Okonjo Iwela, tsohuwar Ministar Kudin Najeriya.

Talla

Kwamitin zaben wanda zai zama shugaban ya aike da sako ga kasashen da ke cikin hukumar cewar sakamakon dalilan halin lafiyar da ake fuskanta da kuma yanayin da ake ciki, wakilan hukumar ba za su iya zama domin yanke hukunci kan wanda zai jagoranci hukumar ta WTO a ranar 9 ga watan nan ba.

Shugaban kwamitin ya ce saboda wadannan dalilai ya dage zaman da kwamitin ya shirya yi har illa masha Allahu domin ci gaba da tuntubar wakilan hukumar domin samun yanayin da ya dace.

Gwamnatin Amurka a karkashin shugaba Donald Trump ta fito karara inda ta bayyana adawarta da takarar Ngozi Okonjo-Iweala wadda ta bayyana a matsayin wadda bata da kwarewar da ake bukata, inda ta bayyana goyan bayanta ga 'yar takarar Koriya ta Kudu.

Ita dai tsohuwar Ministar Kudin Najeriyar na samun goyan bayan kungiyar ECOWAS da Kasashen Afrika da Turai, tare da wasu kasashen Asiya, abin da ake ganin zai bata damar zama shugabar hukumar ta farko daga Afirka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.