Amurka

An fara kiran Biden zababben shugaban Amurka

Shugabar Majalisar Dokokin Amurka Nancy Pelosi ta kira Joe Biden a matsayin zababben shugaban kasar bayan ya samu kuri’u mafi yawa da wani shugaban kasar ya taba samu a tarihi.

Shugabar Majalisar Wakilan Amurka Nancy Pelosi
Shugabar Majalisar Wakilan Amurka Nancy Pelosi REUTERS/Jonathan Ernst
Talla

A jawabin da ta yi na farko bayan zaben, Pelosi ta bayyana yau a matsayin ranar farin ciki ga Amurka, saboda samun shugaban da zai hada kan jama’a.

Pelosi ta ce ya bayyana karara cewar, tikitin Biden da Harris za su kasance a fadar White House, kuma zaben shi abin tarihi ne, wanda ya nuna wagegiyar tazara a tarihin kasar Amurka na kuri’u miliyan 73.8 da kari wanda shi ne kuri’u mafi yawa da wani shugaban Amurka ya taba samu a tarihin kasar.

Shugabar Majalisar ta ce zababben shugaban kasa Biden ya samu goyan baya mai karfi domin yin jagoranci, kuma suna da Majalisar Wakilai mai karfi ta 'yan Democrat da kuma wasu 'yan Democrat da dama a Majalisar Dattawa da za su taimaka masa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI