Amurka

Jiga-jigan Republican na caccakar Trump

Shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump. REUTERS/Carlos Barria

Tsohon dan takarar shugabancin Amurka a Jam’iyyar Republican Mitt Romney ya yi mummunar suka kan shugaba Donald Trump saboda zargin tafka magudi da kuma cewa 'yan Jam’iyyar Democrat na kokarin sace zaben.

Talla

Romney wanda yanzu haka dan Majalisar Dattawa ne a karkashin Jam’iyyar Republican ya ce Trump yana da hurumin gabatar da bukatar sake kidayar kuri’u ko kuma gudanar da bincike dangane da zargin magudin da magoya bayan sa ke zargi akai, amma kuskure ne shi yace anyi magudi ko kuma anyi satar kuri’u.

Sanata Romney ya ce yin haka zai yi matukar illa ga ‘yancin da ake da shi a Amurka da kuma kasashen duniya, yayin da zai kuma yiwa hukumomin dimokiradiya zagon kasa da haifar da mummunar yanayi a cikin kasa.

Romney wanda ya fafata da tsohon shugaban kasa Barack Obama a zaben sa na farko ya dade yana takun saka da shugaba Donald trump da ya fito daga Jam’iyyar sa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.