Covid-19

Duniya ta fara ban-kwana da Covid-19

Kasashen duniya sun kara samun kwarin guiwar kawar da annobar coronavirus sakamakon gano riga-kafinta mai inganci, a daidai lokacin da ake ci gaba da aiwatar da tsauraran matakan yaki da cutar a nahiyar Turai da yankin Gabas ta Tsakiya.

Ana sa ran kimanin mutane biliyan 1 da miliyan 300 su ci gajiyar riga-kafin Fizer nan da badi.
Ana sa ran kimanin mutane biliyan 1 da miliyan 300 su ci gajiyar riga-kafin Fizer nan da badi. Pfizer/PATH
Talla

Samun wannan riga-kafin na Fizer ya sanyaya zukatan kasashen duniya da ke fama da cutar coronavirus wadda a baya-bayan ta kashe fitattun mutane irinsu Saeb Erekat, mai shiga tsakani na Falasdinawa.

A ranar Litinin ne, Kamfanin Harhada Magunguna na Pfizer da BioNTech na Jamus suka sanar cewa, tasirin allurar riga-kafin ya kai kashi 90 cikin 100 wajen hana kamuwa da cutar Covid-19.

Yanzu haka duniya ta samu kwarin guiwar ci gaba da hada-hadarta kamar yadda aka saba a can baya sakamakon gano wannan riga-kafin.

Ana kallon riga-kafin a matsayin wata gagarumar damar karya lagon Covid-19 wadda ta lakume rayuka fiye da miliyan 1 da dubu 200 tare da tilasta dakatar da harkokin yau da kullum a sassan duniya tun bayan farkon bullarta a cikin watan Disamban bara a China.

Pfizer da BioNTech sun ce, za su iya samar da kimanin riga-kafin miliyan 50 a cikin wannan shekara a sassan duniya, sannan kimanin mutane biliyan 1 da miliyan 300 za su iya cin gajiyarsa nan da badi muddin aka amince da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI