Azerbaijan-Armenia

Rasha ta tura sojojinta don samar da zaman lafiya a Karabakh

Yankin Karabakh da ake rikici a kansa tsakanin Armenia da Azerbaijan.
Yankin Karabakh da ake rikici a kansa tsakanin Armenia da Azerbaijan. REUTERS/Francesco Brembati

Rasha ta fara tura sojojinta 2,000 domin aikin samar da zaman lafiya a Yankin Nagorno-Karabakh inda aka kwashe makwanni ana gwabza fada tsakanin Armenia da Azerbaijan.

Talla

Yayin da mutanen Azerbaijan ke murnar tsagaita wutar, a Armenia zanga-zanga aka yi, inda aka bukaci saukar Firaminista Nikol Pashinyan daga kujerarsa.

Yarjejeniyar tsagaita wutar da Rasha ke jagoranci ta ce, za ta tura dakarunta 1,960 da kuma tankunan yaki 90 domin samar da tsaro na shekaru 5 a yankin.

Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan ya ce kasarsa da Rasha za su sanya ido wajen tabbatar da yarjejeniyar tayi aiki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.