EU-Hong Kong

EU ta gargadi China kan dokar da ta kafa a Hong Kong

Kungiyar Tarayyar Turai ta yi kira ga China da ta gaggauta sake nazari kan dokar da ta kafa a Majalisar Dokokin Hong Kong wadda ta yi sanadiyar kawar da kujerun wasu ‘yan majalisa masu rajin tabbatar da demokuradiya.

'Yan Majalisan Hong Kong da aka kora karkashin sabuwar dokar China
'Yan Majalisan Hong Kong da aka kora karkashin sabuwar dokar China REUTERS/Tyrone Siu
Talla

Wannan doka ta China ta raba ‘yan majalisa hudu masu fafutukar tabbatar da demokuradiya a Hong Kong da kujerunsu bayan an yi musu kallon marasa kishin kasa.

Shugaban EU mai kula da manufofin kasashen ketare, Josep Borrell ya bayyana cewa, wannan sabuwar doka ta China za ta dada yin zagon-kasa ga ‘yancin cin gashin kai na yankin Hong Kong.

Kazalika Kungiyar ta Tarayyar Turai ta bukaci a gaggauta mayar da ‘yan majalisan da aka raba da mukamansu.

A jiya Laraba ne mahukuntn Beijing suka aiwatar da sabuwar dokar a Hong Kong wadda ta bai wa shugabar gwamnatin yankin Carrie Lam karfin tsige duk wani dan majalisa da ake kallo a matsayin mara cikakkiyar biyayya, sannan kuma ba shi da damar daukaka kara a kotu.

Jim kadan da samun wannan dama, Lam ta fara aiwatar da karfin ikon kan mutane hudu, amma an samu wasu karin ‘yan majalisa 15 da su ma suka yi murabus domin nuna rashin amincewarsu da dokar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI