Zaben - Amurka

Babu magudi a zaben Biden - Jami'an Zabe

Jami’ai a Amurka suka ce babu wata shaidar da ke nuna an yi magudi a zaben da ya gabata, wanda shugaba mai barin gado Donald Trump ya ki amincewa da shan kaye, a daidai lokacin da China ta aike wa da zababben shugaban kasar Joe Biden sakon taya murna.

Shugaban Amurka mai barin gado Donald Trump
Shugaban Amurka mai barin gado Donald Trump AP Photo/Patrick Semansky
Talla

Bayanan na jami’an na zuwa ne bayan da shugaba mai barin gado Donald Trump ya nanata ikirarin magudin da ya ce an tafka a zaben da ya gabata, duk da cewa ba shi da kwakwarar shaidar zargin da ya yi cewa wata na’ura ta shafe mai kuri’u da suka kai miliyan 2 da dubu dari 7.

A yayin da ‘yan majalisar dokoki daga jam’iyyar Republican ba su kai ga amincewa da nasarar Biden ba, shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa Chuck Schumer, ya zarge su da kau da kai daga gaskiya.

A waje daya kuma, China ta aike da sakon taya murna ga zababben shugaban Amurka Joe Biden, mako guda bayan an bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar, tana mai cewa, ta girmama zabin Amurkawa.

Kafin yanzu, China na cikin wasu manyan kasashen da ba su taya zababben shugaban Amurka murna ba kamar su Rasha da Mexico.

Dangantaka tsakanin Amurka da China ta yi tsami a ‘yan shekarun baya bayan nan a karkashin mulkin shugaba mai barin gado Donald Trump, kuma ba a taba samun haka ba tun da kassashen biyu suka fara hulda a hukumance, shekaru 40 da suka wuce.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI