Coronavirus

Covid-19 ta halaka mutane kusan dubu 10 a rana guda

Sabbin alkaluman hukumar lafiya ta duniya sun nuna cewar jumillar adadin mutanen da annobar coronavirus ta kashe a yau asabar ya kai miliyan 1 da dubu 305 da 39, daga cikin adadin mutane miliyan 53 da dubu 438 da 640 da suka kamu da cutar.

Annobar covid-19 na cigaba da halaka dubban rayuka a kowace rana
Annobar covid-19 na cigaba da halaka dubban rayuka a kowace rana REUTERS/Ciro De Luca
Talla

Sai dai daga cikin wadanda suka kamu da cutar, kawo yanzu mutane miliyan 34 da dubu 324, da 500 sun warke.

A jiya Juma’a kadai, sabbin alkalumman sun ce mutane dubu 9 da 995 annobar ta covid-19 ta aika barzahu, yayinda aka gano karin mutane dubu 660 da 538 da suka kamu da cutar a ranar guda.

Har aynzu Amurka ce kasar da annobar ta fi yiwa ta’adi, inda ta halaka mutane dubu 244 da 364, sai Brazil da ta rasa mutane dubu 164 da 737, yayinda a India annobar ta lakume rayuka dubu 129 da 188, sai kuma Mexico da ta rasa mutane dubu 97 da 624.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI