Ya dace Armenia ta janye daga Nagorny Karabakh cikin kwanaki 10

An cimma yarjejeniya tareda baiwa kasar Armenia dake da dakarun ta yankin Kalbajar dake daf da yankin Nagorny Karabakh wa’adi na kwanaki 10 don ganin ta fice daga yankin da zai koma hanun kasar Azerbaidjan.

Yankin Karabakh  a karkashin ikon Armenia
Yankin Karabakh a karkashin ikon Armenia REUTERS/Francesco Brembati
Talla

An dage lokacin ne zuwa ranar 25 ga wannan wata da muke cikin sa ,biyo bayan cimm a batun tsagaita wuta tsakanin kasashen biyu bayan da Rasha ta kasance a matsayin mai shiga tsakani, bayan da Azerbaidjan ta amince da matakin da aka cimma a wannan yaki da ya lakuma rayukan mutane da dama.

A karshen makon nan Rasha ta yi nasarar jagorantar cimma yarjejeniyar kawo karshen rikicin, wadda a karkashinta Armenia ta amince da mikawa Azerbaijan yankuna da dama a yankin na Nagorno-Karabakh.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI