Birtaniya

Firaministan Birtaniya ya killace kansa saboda corona

Firaministan Birtaniya Boris Johnson ya killace kansa bayan ya yi mu’amala da wani wanda gwaji ya tabbatar ya harbu da cutar coronavirus.

Firaministan Birtaniya Boris Johnson
Firaministan Birtaniya Boris Johnson REUTERS/Toby Melville
Talla

Adadin wadanda wanna cuta ta harba a duniya ya zarce miliyan 54, a yayin da mutane miliyan 1 da dubu 300 suka mutu sakamakon kamuwa da cutar, abin da ya sa gwamnatoci suka sake sanya dokar hana zirga-zirga a yankunansu.

Firaminiista Johnson, wanda ya taba kamuwa da cutar, ya ce yanzu dai garau yake jin kansa, amma ya killace kansa ne don taka-tsantsan biyo bayan mu’amalar da ya yi da wani wanda daga bisasni aka tabatar cutar ta harbe shi.

Johnson ya ce, ya kamata a taka wa cutar biriki daga yaduwar da take yi, yana mai cewa, da kansa zai jagoranci wannan mataki daga fadarsa ta Downing Street.

Wannan killace kai da Johnson ya yi, na zuwa ne a daidai lokacin da ake zangon karshe na tattaunawa cimma yarjejeniyar dangantakar kasarsa da Kungiyar Kasashen Turai bayan raba garin bangarorin biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI