Amurka-Faransa

Ko ganawar Macron da Pompeo na da tasiri?

A wannan Litinin shugaban Faransa Emmanuel Macron ke ganawa da Sakataren Harkokin Wajen Amurka kuma babban na hannun daman Donald Trump, wato Mike Pompeo a birnin Paris. Wannan na zuwa ne a yayin da Macron ya karkata hankalinsa kan sabon zababben shugaban Amurka, Joe Biden domin sabunta hulda da kasar.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron AP Photo/Christophe Ena, Pool
Talla

Tun a ranar Asabar da ta gabata Mista Pompeo ya isa birnin Paris na Faransa a wata ziyarar kwanaki bakwai da ya kaddamar zuwa kasashe aminan Amurka.

Sakataren Harkokin Wajen na Amurka na shan caccaka saboda yadda ya tsaye kai da fata wajen goyon bayan shugaba Donald Trump wanda ya yi zargin tafka makudin zaben da ya sha kaye ba tare da wata hujja ba.

A wata zantawa da ya yi da manema labarai a makon jiya, Mista Pompeo da ya yi mirsisi da sakamakon zaben, ya ce, za a mika mulki zuwa ga gwamnatin Trump karo na biyu ba tare da wata tangarda ba.

Shugabannin kasashen duniya dai ba su yi tantama dangane da wanda suke ganin shi ya lashe zaben na Amurka ba, inda Macron ya kasance a sahun gaba wajen taya Joe Biden murna tare da zantawa da shi ta wayar tarho.

Mista Pompeo ya caccaki yadda ake taya Biden murna, inda ya shaida wa gidan talabijin na Fox News cewa, irin wannan kiran bai dace ba.

Yanzu haka Pompeo na shirin zantawa da Macron a birnin Paris, kuma shi ne ya nemi wannan ganawa da shugaban na Faransa a cewar rahotanni daga fadar Elysee.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI