WHO-Lafiya

WHO ta gamsu da ingancin sabon riga-kafin corona

Hukumar Lafiya ta Duniya ta yaba da ingancin sabuwar allurar riga-kafin cutar coronavirus duk da cewa ta bukatar karin lokaci kafin kammala tantance tasirinsa a jikin dan Adam.

Ana sa ran fara amfni da sabon riga-kafin coronavirus a cikin watan Disamba mai zuwa
Ana sa ran fara amfni da sabon riga-kafin coronavirus a cikin watan Disamba mai zuwa ©MUJAHID SAFODIEN / AFP
Talla

Shugaban Hukumar Lafiyar ta Duniya WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus ya danganta kwayar cutar Covid-19 da zama mummuna da ke farma daukacin sassan jikin dan Adam, yana mai gamsuwa da ingancin sabuwar allurar riga-kafin da kashi 95 cikin 100.

Ghebreyesus ya sanar da taron manema labarai cewa kasashen da ke ci gaba da nuna sakacin yaki da cutar, na wasa ne da wuta  a hannunsu.

A cewarsa, yanzu haka suna ci gaba da samun bayanai masu armashi kan ingancin  rigakafin, sai dai yana da matukar muhimmanci a yi taka-tsan-tsan a lokacin da za a fara amfani da shi a watan Disamba mai zuwa.

Sanarwar da kamfanin Amruka na Moderna ya fitar ta bayyana ingancin riga-kafin da kimanin kashi 95% wajen warkar da cutar ta Covid-19.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI