Birtaniya

Dan ta'addan da Birtaniya ke nema tun 1974 ya shiga hannu

Jami’an tsaron Birtaniya sun kama wani mutum mai shekaru 65 sakamakon rawar da ya taka wajen kaddamar da hare-haren ta’addanci a shekarar 1974 a Birmingham, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 21.

Jami'an 'yan sandan Birtaniya
Jami'an 'yan sandan Birtaniya REUTERS/Kevin Coombs
Talla

Tun da farko dai, an garkame wasu mutane shida a gidan yari bisa kuskuren cewa, suna da hannu a harin wanda aka kai kan gidajen mashaya da ke Birmingham lamarin da kuma ya jikkata mutane 182.

Rundunar ‘yan sandan West Midlands ta ce, dakarun yaki da ta’addanci na Birtaniya tare da takwarorisnu na rundunar ‘yan sandan Arewacin Ireland ne suka yi nasarar cafke mutumin a gidansa da ke Belfast.

An dai kama mutumin ne karkashin dokar yaki da ta’addanci kamar yadda sanarwar rundunar ‘yan sandan ta bayyana, kuma nan kusa za a yi masa tambayoyi a wani caji ofis Arewacin Ireland.

Tagwayen hare-haren da aka kai a ranar 21 ga watan Nuwamban shekarar 1974, sun auku ne a daidai lokacin da tashin hankali ya tsananta na nuna adawa da mulkin Birtaniya a Arewacin Ireland, inda a wancan lokaci aka zargi dakarun wucen gadi na IRA da kai farmakin.

A ranar Asabar mai zuwa ne ake cika shekaru 46 cur da kaddamar da hare-haren bama-baman.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI