Afghanistan

Taliban ta mayar da martani kan shirin Amurka

Kungiyar Taliban ta yi lale marhabin da shirin Amurka na janye dakarunta kimanin dubu 2 da ke Afghanistan, matakin da Taliban ta ce, zai kawo karshen rikicin da kasar ke fama da shi na tsawon shekaru.

Wasu daga cikin mayakan Taliban
Wasu daga cikin mayakan Taliban Reuters
Talla

A jiya ne, Ma’aikatar Tsaron Amurka ta sanar cewa, gwamnatin Donald Trump za ta zabtare yawan dakarun kasar da aka girke a Afghanistan da Iraqi bayan sun kwashe kusan shekaru 20 na yaki.

Sai dai yayin da wasu ke caccakar matakin, ita kuwa kungiyar Taliban ta bakin kakinta, Zabihullah Mujahid ta ce, mataki ne mai kyau wanda zai amfani al’umomin kasashen biyu.

Mujahid ya ce, za a kawo karshen yake-yake da zaran dakarun kasashen waje sun fice daga Afghanistan.

Manazarta dai sun bayyana fargabarsu game da shirin janye dakarun, inda suka ce, matakin zai bai wa Taliban kwarin guiwar ci gaba da cin karanta babu babbaka, sannan kuma tamkar watsar da nasarar da aka samu ne tun shekarar 2001.

Ana sa ran dakarun na Amurka su fice daga Afghanistan nan da ranar 15 ga watan Janairun badi, wato kasa da mako guda kenan da Trump zai mika mulki ga zababben shugaban kasar, Joe Biden.

A karkashin yarjejeniyar da aka cimma a ranar 29 ga watan Fabairun da ya gabata, gwamnatin Trump ta amince ta janye daukacin dakarun ketare daga Afghanistan nan da watan Mayun badi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI