Faransa

Ba na yaki da Islama illa 'yan ta'adda-Macron

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron (Ludovic Marin / POOL via AP)

Shugaba Emmanuel Macron ya zargi Rasha da Turkiya da kokarin dabbaka kiyayyar Faransa a Afrika ta hanyar daukar nauyin mutanen da ke rura kyamar kasar a kafafen yada labarai, yayin da ya jaddada cewa, ko kadan ba ya yaki da Islama.

Talla

Shugaba Macron ya bayyana haka ne a yayin wata hira ta musamman da mujallar Jeune Afrique da aka wallafa a ranar Juma’a, inda yake cewa, ba za su yi rashin azanci ba kan wannan batu kuma akasarin masu sharhi da tsara hotunan bidiyo a kafafen yada labaran Faransanci, na samun tallafin kudade ne daga Rasha da Turkiya a cewarsa.

Macron ya kara da cewa, Turkiya na dada rura wuta kan jawabinsa da aka yi masa gurguwar fahimta dangane da ‘yancin da dokar Faransa ta bai wa masu zanen barkwanci biyo bayan fille kan wani malamin makaranta wanda ya yi batanci ga Islama.

Shugaban ya nanata cewa, yana fada ne da masu muguwar akidar Musulunci, amma sam bai kaddamar da yaki kan addinin Islama ba, illa kurum yana fada da ayyukan ta’addanci a cewarsa.

Gabanin wannan dambarwa, tankiya tsakanin Faransa da Turkiya ta tsananta a watannin baya kan abubuwa da dama da suka hada da batun Syria da Libya da kuma yankin gabashin Tekun Mediterranean.

Faransa ta bukaci Kungiyar Tarayyar Turai da ta sake nazari kan huldar nahiyar da Turkiya wadda a karkashin shugaba Recep Tayyip Erdogan ta gina kimarta a Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.