Zaben - Amurka

Biden zai gabatar da Majalisar Ministocinsa

Shugaban Amurka mai jiran gado Joe Biden
Shugaban Amurka mai jiran gado Joe Biden AP Photo/Carolyn Kaster

Shugaban Amurka mai jiran gado Joe Biden zai bayyana sunayen ministocinsa na farko a ranar Talata, duk da cewa Donald Trump yaki mika kai bori ya hau, ya ci gaba da ikirarin anyi masa magudi ba tare da gabatar da hujjoji ba, yayin da aka fara samun rarrabuwar kawuna cikin jam’iyyarsa.

Talla

Zabebben shugaban na Amurka Joe Biden ya ci gaba da shirye-shiryen karbar ragamar shugabancin kasar daga ranar 20 ga watan Janairu, ba tare da la’akari da yunkurin Trump na bukatan soke sakamakon zaben na Nuwamba ba.

Shugaban ma'aikata na Biden, Ron Klain, ya bayyana hakan ga manema labarai jiya Lahadi, yana mai cewa, za’a san ko su wanene ke majalisar ministocin Amurka daga Talata nan.

Kafofin yada labaran Amurka da dama, ciki har da Bloomberg da The New York Times, sun ruwaito cewa zababben shugaban zai nada gogaggen jami'in diflomasiyya kuma mai taimaka masa na tsawon lokaci Antony Blinken a matsayin sakataren harkokin wajen Amurka.

Shugaba Donald Trump dai har yanzu ya ki mika kai, inda yaci gaba da nuna tirjiya da ikirarin anyi masa magudi da bukatar sake kidayan kuri’un wasu jihohi, duk da watsi da bukatan haka da kotun Pensylvania tayi,to sai dai lauyoyinsa sun sanar da daukaka kara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.