G20

Taron G20 ya amince da taimakawa kasashe matalauta da rigakafin korona

Shugabannin kasashen masu karfin tattalin arzikin duniya G20
Shugabannin kasashen masu karfin tattalin arzikin duniya G20 Presidency Media/Handout via REUTERS

Adadin wadanda suka harbu da cutar korona a duniya ya zarta Million 59, tun bayan bullarta bara a kasar China, yayin da kasashin masu karfin tattalin arzikin duniya G20, Suka sanar da matakin daukar nauyin samar da alurar rigakafin annobar ga kasashe matalauta.

Talla

Kasashe masu karfin tatalin arziki na Duniya G20, a taron kwanaki biyu da kasar Saudiya ta karbi bakwancinsa ta hoton bidiyo, sun bayana cewa zasu dauki nauyin samar da maganin cutar da kuma rarabashi ga kasashe matalauta.

Kasashen sunce dole a samar da isasun kudi a fanin kiyon lafiyar kasa-da-kasa a duniya da kuma inganta bincike kan harkokin kiwon lafiya da magunguna.

Annobar korona data barke a watan Disambar bara a kasar china, yanzu haka ta kama sama da mutane miliyan 59, da 032,742 a sassan duniya, yayin da sama da miliyan 1, 394,389 suka mutu, sai kuma miliyan 40, 792,944 dake amatsayin wadanda suka samu waraka.

Har yanzu kasar Amurka ke kan gaba a kasashen da cutar ta fi yiwa illa, inda sama da mutane 256,725 suka mutu, sai Brazil mai 169,183, sai India da mutane 133,227.

Kanfanin harhada magunguna na kasar Amurka Pfizer da takwaransa na Jamus BioNTech sunyi shelar samar da maganin cutar, inda suke bukatan basu damar fara rarraba shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.