Amurka

Biden ya kaddamar da Majalisar Sakatarorinsa

Zababben shugaban  Amurka Joe Biden
Zababben shugaban Amurka Joe Biden Angela Weiss / AFP

Zababben shugaban Amurka Joe Biden ya kaddamar da kashin farko na Majalisar Sakatarorinsa a daidai lokacin da shirin mika mulki ya kan-kama.

Talla

Muddin aka tabbatar da mutanen da Biden ya zaba, Avril Haines za ta kasance mace ta farko da za ta rike mukamin darekta a hukumar leken asiri, yayin da Alejandro Mayorkas zai zama mutun na farko daga yankin Latin da zai rike mukamin Sakataren Tsaron Cikin Gida.

Tawagar Sakatarorin za ta taimaka wajen samar da ajanda mai taken “Amurka ta dawo wadda ta yi shirin jagorancin duniya” kamar yadda Biden ya bayyana.

Wannan na zuwa ne bayan shugaba mai barin gado Donald Trump ya amince a fara gudanar da shirye-shiryen mika mulki.

Kodayake har yanzu, shugaban ya ki amincewa da shan kaye amma ya ce, dole ne hukumar GSA da ke kula da shirin mika mulki ta aiwatar da abin da ya dace.

Sai dai shugaban ya ci gaba da nanata ikirarinsa mara tushe na cewa, an tafka magudi a zaben na ranar 3 ga watan Nuwamba.

Yanzu haka zababben shugaba Biden zai samu damar damkar miliyoyin Dala da kuma samun bayanan tsaron kasar, sannan zai yi aiki tare da manyan jami’an gwamnatin da za su shirya karbar mulki a ranar 20 ga watan Janairu mai zuwa.

Zababben shugaban ya bayyana bukatar sake gina hulda da aminan Amurka da kuma tunkarar annobar coronavirus da matsalar sauyin yanayi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.