Saudiya-Isra'ila

Saudiya ta musanta karbar bakoncin Firaministan Isra'ila

Sarkin Saudiya Salman bin Abdulaziz.
Sarkin Saudiya Salman bin Abdulaziz. Bandar Al-Jaloud/Saudi Royal Palace/AFP

Rahoton ziyarar Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu a Saudiya Arabia jiya Litinin ya sanya shakkun kan ko kasashen biyu na shirin kulla alakar Diflomasiyya, ko da ya ke masarautar Saudiyan ta musanta batun asirtacciyar ganawa tsakanin Netanyahun da Yarima mai jiran gado Muhammad Bin Salman.

Talla

Cikin sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Saudi Arabia ta fitar wadda Yarima Faisal bin Farhan Al Saud ya wallafa a Twitter ya ce ko kadan Netanyahu bai ziyarci kasar ba bare ma har ya kai ga ganawa da Muhammad bin Salman.

Tun farko dai Netanyahu ya sanar da cewa yana kan hanyarsa daga Tel Aviv zuwa birnin Neom na Saudiya don ganawa da shugabancin kasar ganawa ta farko tsakanin Isra’ilan da Saudiya manyan abokanan gaba masu dogon tarihi.

Kalaman na Netanyahu ya sanya tunanin ko Saudiyan na shirin bin sahun ‘yan uwanta kasashen Larabawa wajen gyatta hulda tsakaninta da Isra’ila da a baya yankin na Larabawa da sauran kasashen Musulmi ke kallo a haramtacciya.

Shugaba mai barin gado na Amurka Donald Trump dai ya yi rawar gani wajen dawo da hulda tsakanin Isra’ila da wasu kasashe larabawa ciki har da hadaddiyar daular Larabawa Bahrain da Sudan a baya-bayan nan.

A ranar 14 ga watan Mayun 1948 ne aka kirkiro kasar ta Isra’ila a tsakar yankin Falasdinawa shekaru 3 bayan kawo karshen yakin Duniya wanda ‘yan Nazi suka kashe yahudawa fiye da miliyan 6.

Matakin kafa kasar ta Isra’ila bisa jagorancin manyan kasashen Duniya ya kai ga fitar da falasdinawa fiye da dubu 760 daga muhallansu wanda ya sanya Larabawa mayar da raddi ta hanyar yunkurin rusa kasar a yake-yake daba-daban har sau 8 a mabanbantan shekaru gabanin Masar ta fara sassautowa tare da kulla yarjejeniyar zaman lafiya da Isra’ilan a 1977.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.