Wasanni

Ana zargin likita da kashe Maradona

Tsohon gwarzon dan wasan duniya dan kasar Agentina Diego Maradona
Tsohon gwarzon dan wasan duniya dan kasar Agentina Diego Maradona Marcos Brindicci/AP Photo

Hukumomin Kasar Argentina sun gurfanar da likitan tsohon tauraron kwallon kafar kasar Diego Maradona a gaban kotu inda ake tuhumar sa da laifin kisan kai,kwanaki 4 bayan mutuwar gwarzon dan wasan.

Talla

Masu gabatar da kara a San Isidro kusa da birnin Buenos Aires sun sanar da cewar Yan Sanda sun kai samame asibiti da gidan Leopoldo Luque domin tattara shaidu.

Binciken ya biyo korafin da ‘yayan Maradona guda 3 suka gabatar da suka hada da Dalma da Giannina da Jana sakamakon irin kular da likitan ya baiwa mahaifin su lokacin da ya gamu da bugun zuciya.

Luque wanda yaki cewa komai kan tuhumar da ake masa, ya wallafa hotan sa da na Maradona lokacin da ya bar asibiti ranar 12 ga watan nan, kwanaki 8 bayan yi masa aiki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.