Amurka

Har yanzu ina kan baka ta cewar anyi mini magudi - Trump

Shugaban Amurka mai barin gado Donald Trump
Shugaban Amurka mai barin gado Donald Trump MANDEL NGAN AFP

Shugaban Amurka mai barin gado Donald Trump yace koda sunan wasa ba zai sauya matsayin sa ba na amsa shan kaye a zaben da akayi wanda yace an tafka magudi domin baiwa abokin takarar sa Joe Biden nasara.

Talla

A wata hira da yayi ta kafar talabijin ta ‘Fox News’, Trump yace babu abinda zai sauya ra’ayin sa akan zargin da yake yanzu har nan da watanni 6 masu zuwa.

Shugaban ya hakikance cewar an tafka magudi a zaben, wanda ya bayyana shi a matsayin rashin gaskiya, inda yake jaddada matsayin cewar shi ne ya lashe zaben cikin sauki.

Hira ta mintina 45 wadda itace ta farko da Trump yayi ta musamman tun bayan shan kaye a zaben da akayi a watan Nuwamba, ta ba shi damar cigaba da korafe korafe dangane da zaben ba tare da gabatar da wata shaida ba.

Duk da sukar zaben da shugaban keyi, har ya zuwa yanzu babu wata gamsashiyar shaidar da lauyoyin sa suka gabatar wanda zai sanya alkalai soke zaben.

Sai dai shugaban ya zargi alkalan da hana jami’an sa gabatar da shaidun da suke da su, inda yake cewa suna da tarin shaidun da zasu tabbatar da zargin da suke yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.