Amurka

Biden ya nada dan Najeriya mataimakin sakataren baitilmali

Shugaban Amurka mai jiran gado Joe Biden.
Shugaban Amurka mai jiran gado Joe Biden. AP Photo/Andrew Harnik

Zababben Shugaban Amurka joe Biden ya zabi wani dan Najeriya Wally Adeyemo a matsayin mataimakin Sakataren Baitulmalin kasar wanda zai yi aiki a karkashin Janet Yellen tsohuwar shugabar Hukumar kudaden kasar.

Talla

Yellen mai shekaru 74 za ta zama mace ta farko da za ta rike mukamin idan Majalisa ta tantance ta, yayin da Adeyemo zai zama dan assalin Afirka na farko da ya zai rike mukamin.

Adeyemo wanda ya rike mukamin tsohon mataimakin mai bada shawara kan harkokin tsaro a gwamnatin Obama, yanzu haka yana rike da mukamin shugaban Gidauniyar tsohon shugaban.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.