Amurka-Biden

Biden ya nada mata zalla amatsayin jami'an sadarwa na Fadar White House

Shugaban Amurka mai jiran gado Joe Biden da mataimakiyarsa Kamala Haris
Shugaban Amurka mai jiran gado Joe Biden da mataimakiyarsa Kamala Haris REUTERS/Mike Blake

Zababben Shugaban Amurka Joe Biden ya gabatar da sunayen tawagar jami’an sadarwar fadar White House, wadda ta kunshi mata zalla, abin da ofishinsa ya kira na farko a tarihin kasar.

Talla

Daga cikin wadanda aka bayyana sunayensu harda Jen Psaki, wacce za ta yi aiki a matsayin sakatariyar yada labarai ta Fadar White House.

Psaki mai shekaru 41 ta rike manyan mukamai da dama a kasar, ciki har da daraktan yada labarai na Fadar White House a lokacin gwamnatin Barack Obama da Biden.

Biden da Mataimakiyar sa Kamala Harris sun nemi shawarwari daga ra’ayoyi maban-banta kan nade-naden da sukeyi na wadanda zasu taimaka musu gabanin rantsar da su a ranar 20 ga watan Janairu mai zuwa wadanda suka fito daga wurare da jinsi ma banbanta.

"Ina alfahari da sanar da ku yau babbar tawagar jami'an sadarwa ta Fadar White House wacce ta kunshi mata zalla," in ji Biden a cikin wata sanarwa da ya fitar.

Baya ga Psaki, an kuma sanar da sunayen wasu matan shida, da suka hada da Kate Bedingfield, wanda ita ce mataimakiyar manajan yakin neman zaben Biden, a matsayin daraktan yada labarai na fadar White House.

Bedingfield ta yi aiki a matsayin daraktan sadarwa na Biden lokacin da yake mataimakin shugaban kasa.

Sauran wadanda aka nada sun hada da Ashley Etienne a matsayin daraktan sadarwa na Harris da Symone Sanders a matsayin babban mashawarcin Harris kuma babban mai magana da yawunta.

Sauran sun hada da Pili Tobar da Karine Jean Pierre da Elizabeth Alexander.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.